Mutum biyu sun mutu a harbin bindiga a Jami’ar Brown ta Amurka

Jami’ar Brown a Amurka ta ba da rahoton mutuwar mutum biyu, tare da jikkatar guda tara dake cikin tsanani a harbin da aka yi a

Jami’ar Brown a Amurka ta ba da rahoton mutuwar mutum biyu, tare da jikkatar guda tara dake cikin tsanani a harbin da aka yi a makarantar.

An ruwaito cewa mutane da yawa sun jikkata a harbin da aka yi kusa da harabar Ivy League da ke Rhode Island.

Hukumomi yankin sun bukaci jama’a da su ci gaba da kasancewa a kulle yayin da maharin ya tsere.

“Zan iya tabbatar da cewa akwai mutane biyu da suka mutu da yammacin yau, kuma akwai wasu mutane takwas da ke cikin mawuyacin hali, kodayake basu cikin damuwa sosai,” in ji Magajin Garin Brett Smiley, a wani taron manema labarai.

“Muna amfani da duk wata hanya da za mu iya don gano maharin in ji Mataimakin Shugaban ‘Yan Sanda Timothy O’Hara.

Wannan harbin shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin hare-haren makarantu a Amurka, inda yunkurin takaita damar malllakar makamai cikin sauki ke fuskantar kalubalen siyasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted