Daruruwan mutanen kasar Somaliya sun fito zanga zangar goyon bayan gwamnatin kasar na korar Hadaddiyar daular Larabawa UAE daga kasar.
Shafin yanar gizo na Africanews ya nakalto majiyar gwamnatin kasar Somalia na cewa a jiya Alhamis ne shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud ya bukaci hadaddiyar daular Larabawa ta fice daga kasar saboda ta gano cewa tana hulda da yankuna guda uku wadanda suke adawa da gwamnatin kasar, kuma sun hada da Somaliland, da yankin Puntland mai neman bellewa da kuma Jubbaland. Kuma tana taimaka masu.
Shugaban ya bukaci jakadan kasar UAE ya bar kasar Somalia a cikin sa’o’ii 72 masu zuwa, sannan ta kira jakadanta da ke Abu dhabi ya dawo gida.