Mutanen Jordan Sun Yi Kira Da A Kawo Karshen Killace Gaza

Mutanen kasar Jordan da su ka gudanar da zanga-zanga a jiya juma’a sun yi kira da a kawo karshen killace yankin Gaza da sojojin HKI

Mutanen kasar Jordan da su ka gudanar da zanga-zanga a jiya juma’a sun yi kira da a kawo karshen killace yankin Gaza da sojojin HKI su ka yi.

Masu zanga-zangar sun bukaci ganin kasashen musulmi da larabawa sun kawo karshen killace Gaza da sojojin HKI su ka yi da kuma laifukan yaki da suke tafkawa.

Daga cikin mahalarta zanga-zangar ta Jordan da akwai sakataren jam’iyyar  “al-hayat”  Abdul-Fattah al-Kailani wanda ya bayyana cewa, Abinda ‘yan sahayoniya suke yi shi ne kokarin fadada yankuwan da suke son mamayewa.”

Al-kailani ya kuma yi kira da a kawo karshen killace yankin Gaza, musamman arewacinsa.

Mutane da dama ne su ka yi zanga-zangar a garin al-kark domin nuna goyon bayansu ga alummar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments