Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa ta sanar da cewa an sami shahidai 12 da kuma wasu mutane da su ka jikkata sanadiyyar kisan kiyashi da sojojin mamaya su ka yi a wurare daban-daban.
Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa ta sanar da cewa an kai gawawwakin shahidai 12 da kuma wadanda su ka jikkata su 41 zuwa asibitocin yankin a cikin sa’o’i 48 da su ka gabata.
Majiyar tashar talabijin din “Mayadin” ta ce, jirgin sama maras matuki na HKI ya kai hari a kusa da shatale-talen al’manara dake gabashin birnin Gaza da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane 4 da kuma jikkata wani adadi mai yawa.
Har ila yau wasu jiragen saman na ‘yan sahayoniya sun kai wani hari a unguwar “ Shuja’iyyah” da ya yi sanadiyyar shahadar mutane 6.
Bugu da kari wasu yankunan da hare-haren na ‘yan sahayoniya su ka shafa sun kunshi; unguwar “Sheikh Ridwan” dake arewa maso yammacin Gaza da unguwar “Karamah” .
Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda su ka yi shahada a cikin shekara daya sun kai 45,553, yayin da wadanda su ka jikkata sun kai 108,379.