Mutanen Da Suka Rasa Rayukansu A Ambaliyar Nepal Sun Kai 750

Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a ambaliyar kasashen Nepal da China suna kara yawa. Kamfanin dillancin labarai IP na kasar Iran ya bayyana cewa

Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a ambaliyar kasashen Nepal da China suna kara yawa.

Kamfanin dillancin labarai IP na kasar Iran ya bayyana cewa zuwa safiyar yau Lahadi yawan wadanda suka mutu ya kai 750 sannan wasu akalla 3000 sun bace.

Hukumomi a Nepal sun bayyana cewa a halin yanzu sun maida hankali kan daruruwan ma’aikata da ba’a san halin da suke ciki ba a madatsar ruwa ta bada wutan lantarki a kan kogin Himalaya, wadanda duwatsun kankara suka fada a kansu.

Labarin ya kara da cewa an dakatar da aikin ceto nawani lokaci a cikin yan kwanakin da suka gabata saboda lalacewar yanayi a yankin. Saboda kuma tsoron wata ambaliyar zata iya aukuwa saboda ruwan da ya taro a wani wuri tsakanin Nepal da yankin Tibet na kasar China.

Labarin ya kara da cewa har yanzun mutane 290 ne suka bace a kasar Indiya saboda wannan ambaliyar ruwa.

Sannan a yankin Tibet na kasar China kuma ana ci gaba da neman wadanda suka bace.

Kungiyar red Cross ta ce mai yuwa waranda abin ya shafa a ambaliyan ruwan zai kai 90,000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted