Jami’an gwamnati a yankin Ireland sun bada sanarwan cewa gidaje da wuraren ayyuka kimani 725,000 ne basa da wuta saboda guguwar iska wacce ta yi sanadiyyar lalata kayakin lantar masu yawa a yankin.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa masana sun bayyana guguwar da suka bawa suna ‘Eowyn’ a matsayin guguwa mafi karfi a tarihin kasar.
Hukuma mai kula da wutan lanatarki a kasar ta bayyana cewa iskar mai saurin kilomita 160 a ko wace sa’aa ta yanke wutan lantarki a yankuna da daman a kasar, kuma basu taba tsammanin irin wannan guguwar a wannan lokacin ba.
Labarin ya kara da cewa har yanzun akwai tsaron wannan guguwar zata ci gaba da barna a cikin kasar a yainda yake wucewa.
Kamfanin wutan lantarkin ya bayyana cewa mai yuwa a dauki mako guda kafin a maida wutan lantarki a dukkan fadin kasar Burtani da kuma tsibiranta.
Labarin ya kara da cewa yawan barnan da guguwar tayi a arewacin Island ya kai gidaje 240,000.
Sanadiyyar wannan guguwar dai an dakatar da sauka da tashin jiragen sama da kananan jiragen ruwa a arewacin Islanda da kuma Burtania zuwa lokacinda guguwar zata wuce kasar.