Mutane A Birnin Tehran Sun Koma Kan Rayuwarsu Da Suka Saba

Bayan tashe-tashen hankula wadanda suka mamaye kasar Iran saboda yan ta’adda wadanda Amurka da HKI suke taimakawa a cikin kasar a halin yanzu mafi yawan

Bayan tashe-tashen hankula wadanda suka mamaye kasar Iran saboda yan ta’adda wadanda Amurka da HKI suke taimakawa a cikin kasar a halin yanzu mafi yawan harkokin rayuwa sun koma kamar yadda suke a birnin Tehran da sauran birani a kasar.

A ranar 12 ga watan Jenenrun da muke ciki aka fara zanga-zangar lumana a babbar kasuwar birnin Tehran, inda suke neman gwamnatin kasar ta shiga don kyautata rayuwarsu da kuma harkokin kasuwancinsu saboda yadda tashin farashin kayayyaki ya rikata harkokin kasuwancinsu.

Amma a ranakun 8 da zuwa 10 na watan Jeneru yan ta’adda wadanda suke samun goyon bayan amurka da HKI suka shiga cikin masu zanga-zanga inda suka maida ita tashe-tashen hankula wanda ya kai ga kashe-kashe masu yawan da kuma lalata dukiyoyi da masallatai da kona alkur’ani mai girma.

Amma bayan shigowar mutanen gari suka kuma kawo karshen tashe tashen hankula tare da taimakon jami’an tsaro a halin yanzu nutsuwa ta koma kan mafi yawan kasar kuma rayuwa tana tafiya kamar yadda aka saba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted