Mutane 7 Sun Mutu A Wani Hari Da Aka Kai Kan kasar Siriya

akalla mutane 7 ne suka mutu a wani hari da aka kai a wata bus a tsakiyar kasar siriya

Rahotanni daga kasar siriya sun bayyana cewa harin da aka kai kan wata motar bus  a tsakiyar siriya yayi sanadiyar mutuwar mutane 7 , yayin da wani harin da aka kai kuma ya shafi babban bututun iskar gas kusa da babban birnin kasar, lamarin da ya haifar da dakatar da ayyukan cibiyoyin samar da wutar lantarki guda 3, da kuma kara sanya matsin lamba kan muhimman kayayyakin more rayuwa a kasar.

Kamar yadda kafafen yada labaran kasar siriya suka bayyana  wasu masu dauke da makamai da ba’asan ko su waye ba sun bude wuta kan wata motar bus a tsakiyar lardin Homs  kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 7 tare da jikkata wasu guda 4, kuma mutane dake cikin motar akwai injiniyoyi da kuma sauran ma’aikata dake aiki da kamfanoni masu zaman kansu da kuma ma’aikatan kamfanin wutar lantarki ta kasar siriya

Wannan harin shi ne na baya bayan nan a yunkurin da ake yi na tada hargitsi tsakanin bangrori marasa rinjaye da kuma ma’aikatan gwamnati tun bayan rushewar tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta bashar Asad,  a shekara ta 2025  yankin dake gabar teku yana dauke da mafi yawan yan alawiyya dake zaune a wajen  kuma suke fuskantar hare hare da kisan kare dangi inda sama da mutane 1400 suna mutu

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted