A cigaba da hare-haren wuce gona da iri da sojojin HKI suke yi a kasar Lebanon, mutane 6 ne su ka yi shahada yayin da wasu 17 su ka jikkata.
Wannan adadin na wadanda su ka yi shahada ya kasance a garin “Wardaniyya” da jiragen yakin HKI su ka kai hari akan hotel din “Darussalam dake dauke da ‘yan gudun hijira.
Magajin garin, Ali Buraim ya bayyana cewa; harin na HKI ya yi sanadiyyar rusa wani gini mai hawa 4 da aka ware shi domin karbar masu hijira da su ka baro gidajensu sanadiyyar yaki.
Wasu garuruwan da sojojin HKI su ka kai wa hare-hare a kudancin Lebanon, sun hada “Yadir, al-Hush, al-Suldaniyya, Arabsalim, Dab’al, da kuma Jabal-al-Rafii. Sai kuma garuruwan Biladh, Tabnin, Majadal Salam, Qalawiyah, al-Bazuriyyah, Naqura, da kuma Aitit.
Bugu da kari, da marecen yau jragen HKI sun kai wasu hare-haren akan garuruwan da su ka hada Jibshit, shaba’a, al-Hushg, Dalun, da Habshu.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta ce, a jiya Laraba mutanen da su ka yi shahada sun kai 22 da hakan ya sa jumimmar shahidai ya ka 2,141, sai kuma wadanda su ka jikkata da su ka kai 10099.