Rahotanni suna cewa akalla mutane 4 sun jikkata bayan fashewar wasu bama bamai a wajen adana makamai da kayayyakin soji a birnin Aleppo dake arewacin kasar siriya, kuma tuni jami’an tsaro na farar hula suka kwashe mutane da gidajensu dake kusa da wajen.
Gwamnan birnin Aleppo Azzam Al-gharib yayi kira ga mutane da kada su bar gidajensu a halin yanzu , yace motocin daukar marasa lafiya da masu bada agajin gaggawa suna cikin shirin ko ta kwana don bada agaji.
irin wannan fashewar abubuwa din ya faru a kwanakin baya a kasar inda yayi sanadiyar mutuwar mutane 11 a bangren barikin soja a yankin ayyash dake lardin dayr al-zawr na kasar siriya
tun bayan kifar da gwamnatin bashar asad a farkon watan decembar shekara ta 2024 sojojin isra’ila suk kaddamar da muggan hare hare kan muhimman kayayyakin soji da wuraren adana makamai,wanda ke karkashin ikon sojojin Syriya