Mutane 25 Sun Mutu Wasu 40 Kuma Suka Jikkata A Yamen

hare haren saudiya yayi sanadiyar kashe mutane 25 da kuma jikkata wasu guda 40

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin kasar saudiya sun kaddamar da hare hare a wata kasuwa a lardin Taizz dake kudu masu yammacin kasar  yamen kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 25 tare da jikkata sama da 40, kasa da makon daya ke nan da dakarun kasar saudiya suka kai hari kan wata kasuwa a lardin

Kakakin rundunar sojin kasar Yamen brigadier janar yahye Saree ya bayyana cewa  jirgin sama mai lamba F-15sa na kasar saudiya  da ya taso daga sansanin jirgin sama na sarki khalid dake kusa da khamis mushait dake kudu masu yammacin kasar saudiya ya kai hari da safiyar yau a wurare 3 a wata kasuwa a kasar yamen

Haka zalika ya kara da cewa hare haren na saudiya ba zai tafi hakan nan ba tare da mayar da martani ba, ma’aikatar lafiya ta yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu na kara karuwa adaidai lokacin da halin wadanda suka jikkata suke cikin mawuyacin hali

Ma’aikatar kare hakkin bil adama ta kasar yamen ta yi tir da harin da saudiya takai a kasuwa , yace kai hari kan fararen hula kai tsaye ya sabama dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar janeva mai lamba 52

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted