Tsohon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Dr. Muhsin Riza’i ya bayyana cewa; Shugaban Kasar Amurka Donald Trump da Fira ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamine Netanyahu suna kokarin kunna wutar yakin duniya na uku bisa la’akari da yadda su ka yaki Falasdinu, Lebanon,Syria, Qatar, Iran da Venezuela.
Muhsin Riza’i ya kuma bayyana yadda shugaban kasar Amurka Donald Trump yake yin barazanar yaki ga kasashen Mexico, Cuba, Columbia, kuma har da abokan Amurka na turai kamar kasar Denmark.
Haka nan kuma tsohon kwamadan dakarun kare juyin musulunci “IRGC” ya yi Ishara da yadda shugaban na kasar Amurka ya tayar da rashin jituwa a tsakanin kasashen Rasha da kasashen turai, da kuma a tsakanin China da Japan, da tsakanin Korea ta Kudu da ta Arewa.
Dr. Muhsin Riza’i ya kuma ce idan har kungiyoyin duniya ba su takawa Trump da Netanyahu birki ba, to za a yi yakin duniya na uku.
Tsohon kwamandan dakarun kare juyin musuluncin na Iran ya kuma ce, wadannan wawayen mutane ba su san cewa idan aka yi yakin duniya na uku ba, to su ma ba za su tsira ba.
Dr. Muhsin Riza’i ya kuma yi bayani akan yadda makiya su ka sha kashi a hannun Iran a lokacin yakin kwanaki 12, sannan ya kara da cewa, bayan wancan abinda ya farun ne su ka fito da Karin matsin lamba akan Iran domin haddasa sabani a tsakani gwamnati da kuma al’ummar kasar.
Haka nan kuma ya jadda cewa; Al’ummar Iran za ta sami galaba akan Netanyahu da kuma Trump.