Tarayyar Turai Tana Shirin Yin Fito Na fito Da Donald Trump Na Amurka

Jaridar Politico wacce ake bugawa a Amurka ta nakalto wani jami’in diplomasiyyar turai wanda ya bukaci a sakaya sunansa yana cewa; Tarayyar turai din tana cikin Shirin kalubalantar shugaban Amurka Donald Trump matukar ya kwace iko da yankin Greenland na kasar Denmark. Jami’in diplomasiyyar na turai ya kuma ta fara tattauna fito da tsarin da […]
Jagora: Iran Ba Za Ta Yi Kasa A Gwiwa Ba Wajen Fuskantar Mabarnata

Jagoran Juyin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa, ko kadan kasar ba za ta yi sassauci wajen fuskantar mabarnata ba. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a yau Jumaa a yayin karbar bakuncin dubban mutanen da su ka kawo masa Ziyara daga birnin Qum, ya kuma ce; “Ya […]
Ministan Tattalin Arziki Na Lebanon Ya Jaddada Wajabcin Bunkasa Harkokin Kasuwanci Da Iran

Ministan tattalin arziki na Lebanon Amir al-Bisat ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakunci ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci a birnin Beirut,wanda kuma ya sami halartar babban jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran din akan tattalin arziki da kasuwanci. A nashi gefen ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Abbas Arakci ya […]
Muhsin Riza’i: Trump Da Netanyahu Suna Kokarin Kunna Wutar Yakin Duniya Na Uku

Tsohon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Dr. Muhsin Riza’i ya bayyana cewa; Shugaban Kasar Amurka Donald Trump da Fira ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamine Netanyahu suna kokarin kunna wutar yakin duniya na uku bisa la’akari da yadda su ka yaki Falasdinu, Lebanon,Syria, Qatar, Iran da Venezuela. Muhsin Riza’i ya kuma bayyana […]
An Karyata Labarin Dake Cewa An Rufe Filayen Jiragen Saman Iran

Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Iran ta fitar da sanarwa da take karyata cewa,an rufe filayen jiragen saman kasar, tare da tabbatarwa da matafiya su rika tuntubar hanyoyin da su ka dace domin samun bayanai masu inganci. Hukumar ta kuma ce; Abin takaici ne yadda wasu kafafe suke watsa kirkirarrun labarai dangane da zirga-zirgar jiragen […]