Muhajirani: Abokan Gaba Suna Son Raunana Iran Da Karkatsata

Mai Magana da yawun gwamnatin Iran Malama Fatima Muhajirani ta bayyana cewa; Abinda gwamnati ta mayar da hankali akansa a wannan lokacin shi ne hana

Mai Magana da yawun gwamnatin Iran Malama Fatima Muhajirani ta bayyana cewa; Abinda gwamnati ta mayar da hankali akansa a wannan lokacin shi ne hana afkuwar yaki, da kuma fuskantar makarkashiya, da take nufin karkatsa Iran da raunanata.

Muhajirani wacce ta gabatar da taron manema labaru a yau Talata ta kuma ci gaba da cewa; masu sayar da mafarkin tsaye da kuma makiya ‘yan waje, babu wani abu da za su iya yi wa kasarsu, domin duk manufarsu daya wacce ita ce tarwatsa Iran da mayar da ita mai rauni. Amma da falalar Allah da himma ta al’umma, da kuma dogaro da hikima da hankali, za su fita daga cikin Zangon.

Kakakin gwamnatin ta Iran ta kuma kara da cewa; A halin yanzu ana gudanar da cikakken bincike akan abubuwan da su ka faru a bayan nan a tsakanin ranakun 8 zuwa 9 ga watan Janairu 2026; sannan kuma ta kara da cewa; Ta hanyar dogaro da aiki da hankali da yardar al’umma, da kuma yin furuci da aikata kura-kurai, za su tsallake wannan Zangon da falalar Allah madaukakin sarki.

Akan fagen diplomasiyyar Iran kuwa, Malama Fatima muhajirani ta ce; Iran ta gina alaka mai karfi da kasashen kungiyoyin Brics da Shagahai da kuma kasashen makwabta, don haka duk da takunkuman da aka kakabawa Iran din, Iran tana samun ci gaba a fagagen kere-kere da ilimi.

Bugu da kari, Muhajirani ta ce; Diplomasiyya da matakan kandagarko na soja da Iran take dauka wasu muhimman dabaru ne da suke tafiya kafada da kafada domin kare manufofin kasa da daukakarta.

Da take Magana akan ‘yan sahayoniya, Muhajirani ta bayyana su da cewa; Su ne Magolawan wannan zamanin, tana mai cewa; Iran ta iya samun nasarar gina hasumiyar nazarari da bincike ta sararin samaniya ta ” Muragah” a Azerbaijan wanda ci gaba ne na ilimi na koli duk da yake-yaken Magolawa.

Kakakin gwamnatin ta Iran ta kuma ce; Gwamnati tana bayyana mahangarta ne bisa dogara da aiki da hankali da kuma tattaunawa, kuma mun yi Imani da cewa babu yadda za a iya gina ci gaba sai ta hanyar dogaro da hankali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted