Rahotannin da suke fitowa daga kasar Moroko sun ce ruwa kamar da bakin kwarya da yake sauka a yankunan arewacin kasar, ya sa an dauke mutanen da sun kai 150,000 zuwa wasu yankuna na daban.
A garin Ould Ameur an rika yin kira ga mutane ta amsa amon masallaci da su gaggauta ficewa daga garin, saboda yadda mamakon ruwan sama yake sauka.
Wata mace mai suna Kasia El-Selami ta fada wa manema labaru cewa daga lasfikar masallaci ya ji ana yin kira ga mutane da su yi saurin barin garin.
Selami ta ci gaba da cewa; Mun ji tsoro nan take,musamman saboda muna da yara hudu.
Ya zuwa yanzu dai an sanar da cewa mutane 4 sun kwanta dama sanadiyyar ambaliyar ruwan saman daga cikinsu da akwai karamin yaro dan shekaru biyu, kuma har yanzu ana neman wani mutum daya da ya bace,kamar yadda mahukunta a yankin su ka ambata.
An ga wasu mutanen yankin da su ka hada kananan yara da tsofaffi suna tsaye akan rufin gidajensu, bayan da ruwa ya malale cikin gidajen nasu.
Mahukunta sun kai dauki zuwa yankin inda aka yi amfani da kwale-kwale domin dauke mutanen yankin zuwa inda za su sami matsugunni.
A yankin Kenitra mai nisan kilo mita 50 daga Arewacin Rabat, an shirya matsugunin ajiye mutanen da sun kai 40,000.
A watan Disamba ma mutane 37 su ka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwan sama a Safi da ya zama asarar mafi girma ta rayuka da aka yi a cikin kasar ta Moroko a cikin shekaru 10 sanadiyyar ibtila’i na dabi’a.
A kasar Aljeriya mai makwabta da Moroko ma, an sanar da mutuwar mutane biyu, da su ka hada da karamin yaro.
A kasar Tunisia, mutane 5 ne aka sanar da rasuwarsu.
An sanar da cewa a cikin shekaru 70 da su ka gabata, wannan shi ne ruwan sama mafi yawa da ya sauka a wannan yankin na arewacin Afirka.