Mokhber:  Dole ne kasashen musulmi su hada kai don dakile laifukan Isra’ila a Gaza

Shugaban rikon kwarya na kasar Iran Mohammad Mokhber ya bukaci hadin kan kasashen musulmi domin kawo karshen yakin kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar

Shugaban rikon kwarya na kasar Iran Mohammad Mokhber ya bukaci hadin kan kasashen musulmi domin kawo karshen yakin kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza.

Mokhber ya yi wannan tsokaci ne yayin da yake magana ta wayar tarho da firaministan Pakistan Shehbaz Sharif a ranar Lahadi.

Shugaban na rikon kwarya na Iran ya yaba da irin goyon bayan da al’ummar Pakistan suke yi wa Falasdinawa a Gaza da kuma irin matakin da gwamnatin Pakistan ta dauka kan laifuffukan da yahudawan sahyoniya suke yi a yankin da aka killace.

Mokhber ya jaddada cewa ya zama wajibi ga dukkan kasashen musulmi su hada kai don hana ci gaba da laifukan sahyoniyawa a Gaza.

A wani bangare na jawabin nasa, shugaban rikon kwarya na Iran ya yi Allah wadai da yaki da tashe-tashen hankula da kuma ta’addanci, tare da bayyana hakan a matsayin wata hanya da kasashe masu girman kai suke amfani da ita domin zaluntar al’ummomi raunana a duniya.

Mokhber ya kuma tabo yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin Tehran da Islamabad a ziyarar da marigayi shugaban kasar Iran Ebrahim Raeisi ya kai Pakistan.

Ya kuma bayyana cewa, kasashen biyu sun amince da kara yawan musayar ciniki da tattalin arziki zuwa dala biliyan 10 a duk shekara, ya bayyana fatan cewa, za a cimma wannan muhimmin buri ta hanyar kokarin da kasashen biyu ke yi da kawar da shingayen kasuwanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments