Mohajerani: Iran Tana Neman Zaman Lafiya Mai Daurewa A Yankin

Kakakin gwamnatin Iran ta bayyana cewa: Suna neman zaman lafiya mai daraja kuma ba za su yi jinkirin kare ƙasarsu ba Kakakin gwamnatin Iran ta

Kakakin gwamnatin Iran ta bayyana cewa: Suna neman zaman lafiya mai daraja kuma ba za su yi jinkirin kare ƙasarsu ba

Kakakin gwamnatin Iran ta jaddada cewa: Kare muradun ƙasa da kare haƙƙin yankin ƙasar su ne manyan abubuwan da gwamnati ta sa a gaba, tana mai cewa: “Neman zaman lafiya mai daurewa ba ya nufin yin sakaci da buƙatar tsaron ƙasa.”

A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, kakakin ta tabbatar a yayin wani taron manema labarai cewa: Fifikon gwamnatin yanzu shine magance yanayin rayuwar ‘yan ƙasa.

Ta bayyana cewa gwamnati ta himmatu wajen magance ƙalubalen tattalin arziki da jama’a ke fuskanta da kuma ƙoƙarin inganta walwala gaba ɗaya, tare da mai da hankali kan kare rayuwar iyalai da biyan buƙatunsu na asali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted