Ministocin Tsaron kasashen Rasha Da JMI Sun Hadu A Birnin Mosco

Ministocin tsaro na kasar Rasha ta JMI sun hadu a birnin Mosco don tattauna batun karfafa dangantakar tsaro a tsakaninsu a dai dai lokacinda al-amuran

Ministocin tsaro na kasar Rasha ta JMI sun hadu a birnin Mosco don tattauna batun karfafa dangantakar tsaro a tsakaninsu a dai dai lokacinda al-amuran tsaro suke kara tabarbarewa a yankin kudancin Asiya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jakadan kasar Iran a Mosco yana fadar haka.

Kazem Jalali, ya bayyana cewa kasashe biyu suna kara zurfin dangantakarsu da juna a dai-dai kasashen biyu suke kara fuskantar matsinn lamba daga kasashen yamma musamman Amurka, da kuma HKI.

Kasashen biyu sun ga yakamata su kara dankon zumunci a tsakaninsu a fagen tsaro, bayan yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorowa kasar Iran.

A wannan zuwan dai ministan tsaron JMI ya raka Dr Ali Larijani babban mai bawa jagoran juyin njuya hali musulunci shawara a ganawarsa da shugaba Vladmir Putin a fadar Krimlin a ranar Lahadi.

Kazem Jalali, ya bayyana cewa a wannan karon ma bangarorin biyu sun tattauna baton karfafa dangantakar tsaron kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted