Jamhuriyar Nijar na karbar bakuncin taron ministocin harkokin wajen kasashen kawancen Sahel da Rasha a Yamai.
Taron wanda shi ne karo na biyu na shawarwarin diflomasiyya tsakanin Tarayyar AES da Rasha, na da matukar muhimmanci ga kawancen biyu.
Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Ravrov, ya kasance tare da takwarorinsa uku daga Nijar, Burkina Faso, da Mali.
Kamar yadda aka yi a zaman da ya gabata, tattaunawar ta Yamai za ta taimaka wajen karfafa nasarorin da aka samu da karfafa diflomasiyya, ci gaba, da kuma tsaro a nan gaba.
Kafin zuwansa Nijar, Minsitan Harkokin Wajen Rasha SergeiLavrov ya ce zai je ne don halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen uku da nufin kulla dangantaka mai karfi tsakanin kasashen na Sahel da Tarayyar Afirka, Bayan tattaunawarsa da Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahamad Ali Youssouf a Habasha a ran gadin da ya soma a Afrika.
A yayin tattaunawar, bangarorin biyu sun amince su gudanar da shawarwarin siyasa na shekara-shekara.
Ministan Harkokin Wajen Rasha ya tabo matsalolin tsaro da ke faruwa a yankin Sahara da Sahel, da Kahon Afirka, da kuma a Sudan, da Sudan ta Kudu, da kuma Libya inda ya bayyana cewa Moscow za ta ci gaba da tallafawa abokan huldarta na Afirka wajen warware wadannan rikice-rikice.
Wannan sabon zagayen tattaunawa tsakanin Kasashen Sahel da Tarayyar Rasha ya zo ne a daidai lokacin da Ƙungiyar ke bikin cika shekaru biyu da kafuwarta.