Search
Close this search box.

Ministan Yakin Isra’ila Ya Yi Murabus Daga Gwamnatin Netanyahu

Ministan yaki na Isra’ila, Benny Gantz, ya sanar da murabus dinsa daga gwmanatin Netanyahu, saboda abinda ya kira bambance-bambance a yadda ake tafi da al’amura,

Ministan yaki na Isra’ila, Benny Gantz, ya sanar da murabus dinsa daga gwmanatin Netanyahu, saboda abinda ya kira bambance-bambance a yadda ake tafi da al’amura, game da yakin Gaza.

Gantz na mai da’awar cewa Netanyahu “ya hana su cimma ainihin nasara” a yakin da suke a Gaza.

Yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai jiya Lahadi, Mista Gantz ya ce firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bari a samu abin da ya kira ‘tabbatacciyar nasara’ kan Hamas.

A daya bangaren kuma ministan ya kara da cewa dole ne Mista Netanyahu ya sanya ranar da za a gudanar da zabukan kasar.

Dama dai tun cikin watan Mayun da ya gabata, Benny Gantz ya yi barazanar yin murabus daga majalisar yakin kasar idan Netanyahu ya ki bayyana shirinsa na kula da zirin Gaza bayan yakin da suke yi da Hamas.

Firaministan Benjamin Netanyahu ya yi kakkausar suka ga Benny Gantz saboda murabus daga gwamnatinsa.

Netanyahu ya fada a wani sako da ya wallafa a X cewa ”Bany, yanzu ba lokaci ne na watsi da yakin ba, lokaci ne na hada karfi waje guda.”

Shi ma wani mai sa ido a majalisar ta yaki, Gadi Eisenkot, wanda wani tsohon shugaban ma’aikata ne a rundunar sojan Isra’ilar, ya sanar da murabus dinsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments