A matakin farko na mayar da martani akan abinda ya faru, Ministan tsaron kasar ta Venezuela Vladimir Padrino López ya sanar da shiga halin ko-ta-kwana a fadin kasar.
Haka nan kuma ya ce; kasar za ta yi aiki da dukkanin karfin da take da shi domin kare ‘yancinta da huruminta.
Ministan tsaron na kasar Venezuela Vladimir Padrino López wanda janar ne mai taurari 4, ya gabatar da jawabi ne ta kafar talbijin da aka watsa da safiyar Asabar 3 janairu 2026, ya kuma bayyana harin na Amurka da cewa: Shi ne mafi muni da Amurkan ta kai wa kasarsa, kuma suna kirga adadin wadanda aka kashe da kuma wadanda su ka jikkata.
Minista Vladimir Padrino López ya kuma ce: “Mahara bakin haure sun kawo wa kasarmu mai tsarki hari a cikin Fuerte Tiuna,Caracas, Jahar Miranda, Aragua, da La guira.”
Haka nan kuma ya ce; Za su sami nasara a cikin wanann fadan,domin za su yi gwagwarmaya.
Wani sashe na jawabin ministan tsaron kasar taVenezuela ya kunshi yin kira ne ga al’ummar kasar da kar su ji tsoro, su kuma kaucewa fadawa cikin rudani a wannan yanayin na hare-haren Amurk. Domin abinda abokan gaba suke so shi ne su jefa mu a cikin rudani.
Dangane da rundunar sojan kasar, Ministan tsaron kasar ta Venezuela ya ce suna cikin Shirin ko-ta-kwana da jan damara, domin kare kasar.