Ministan Tsaron JMI Ya Ce Makiya Zasu Sha Mamaki Idan Sun Keta Sararin Samaniyar Kasar

Ministan tsaron kasar JMI ya bayyana cewa kasarsa ta na da karfin garkuwan kare sararin samaniyar kasar mai karfi, sannan hakama a bangaren sojojin ruwa.

Ministan tsaron kasar JMI ya bayyana cewa kasarsa ta na da karfin garkuwan kare sararin samaniyar kasar mai karfi, sannan hakama a bangaren sojojin ruwa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgediya Janar Aziz Nasir-zadeh ya na fadar haka a yau Litinin, a lokacin biki na musamman, na mikawa sojojin kasar sabbin jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kimani 1000 guda, don amfani da su a duk sanda a ke bukatar amfani da su don tsaron kasar daga makiya.

Ya kuma kara da cewa, karin wadannan jiragen yaki kan wadanda sojojin kasar suke da su, zai kara karfafa tsaron sararin samaniyar JMI.

Janar Nasir Zadeh ya kara da cewa sabbin jiragen da suka shigo hannun sojojin a yau suna iya sauka su sake tashi a ruwa, sannan zasu yi aiki a yakin kan tudu a duk inda ake bukatarsu. Har’ila yau suna aiki da fasahar zamani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments