Ministan tsaron kasar Jamus wanda yake Magana akan halin da gabas ta tsakiya take ciki da harin wuce gona da iri na Amurka akan Iran ya ce, Iran tana da karfi sosai, kuma sun yi yaki cikin kwarewa domin kare kasarsu.
Ministan tsaron kasar ta Jamus wanda tashar talabijin din “Fox news” ta yi hira da shi akan halin da ake ciki a gabas ta tsakiya ya ce, ya zuwa yanzu babu tabbacin inda aka dosa ko abinda zai iya faruwa a gaba,amma dai a fili yake cewa Iran tana da karfi sosai.
Ministan tsaron kasar ta Jamusu Boris Pistorius ya kuma ce; Abin takaici a halin yanzu an sake samun wani tashin hankali a tekun “Red Sea” bayan mashigar Ruwan “Hurmuz.”
Boris Pistorius a halin yanzu muna da bukatuwa da a lalubo hanyoyin warware matsalarr tattalin arziki da duniya take fuskanta.
Da yake Magana akan batun inshore na man fetur da Gas, a cikin turai akan gaba, ministan tsaron na kasar Jamus ya ce; A halin yanzu muna ganin yadda farashin makamashi yake karuwa domin kowace lita ta man fetur ta kusa kai Euro 2.5 wanda hakan Babban kalubale ne ga mutanen dake aiki a cikin Jamus da kuma Amurka.
Akan yakin Ukiraniya kuwa, ministan tsaron na Jamus ya zargi Rasha da cewa tana fada ne da kasashen Nato.
Da ya tabo batun janye sojojin Amurka daga kasarsa,ministan na kasar Jamus ya ce ko kadan hakan bai shammaci Jamus ba.
.