Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya jaddada cewa, a yakin baya-bayan nan da aka kallafa wa kasarsa ba su yi amfani da manyan makaman da kasar take mallaka ba.
Janar Nasirzadeh ya bayyana cewa, a wannan yakin, Iran ta fuskanci barazana bayan da kasa mafi karfin soji a duniya wato Amurka, da kuma wasu manyan kasashen turai suka shigar wa Haramtacciyar Kasar Isra’ila a yakin da ta kaddamar kan Iran, amma duk da haka basu samu damar sarrafa fagen daga yadda yake so ba.
Ministan tsaron kasar ya bayyana cewa, daga cikin manyan nasarorin da Iran ta samu da taimakon Allah a cikin kwanakin yakin, akwai nasarar sarrafa sararin samaniya, da aiwatar da ayyuka na soji masu sarkakiya da suka dagula lissafin da makiya suka yi tun daga afrko.
A yanzu kuma ya bayyana cewa akwai wasu nasarorin da kasar ta samu ta fuskar ayyuka da dama a fannin kera tauraron dan adam, da kera na’urori masu inganci da nagarta na zamani, wanda masana na kasar ne da kansu suke gudanar da aikin bisa jajircewa da kumaji wajen yin aiki tukuru a dukanin fagage.