Kafofin yada labaran Isra’ila sun sanar da cewa: Ben Gvir ya sanar da yin murabus daga gwamnatin Netanyahu
Jaridar Haaretz ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta nakalto a jiya Asabar cewa: Ministan tsaron Isra’ila Itamar Ben-Gvir ya sanar da yin murabus daga gwamnatin Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila ta Benjamin Netanyahu, domin nuna adawa da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.
Jaridar Al-Quds Al-Arabi ta ce: A daidai lokacin da ministan kudi na haramtacciyar kasar Isra’ila Bezalel Smotrich ya tabbatar da aniyar Netanyahu na mamaye Zirin Gaza sannu a hankali, tare da mayar da yankin, inda ba za a sake rayuwa a ciki ba, sai kuma ga wannan sabon lamari ya faru.
Ben-Gvir wanda kuma shi ne shugaban jam’iyyar Otzma Yehudit mai ra’ayin rikau, ya bayyana a jiya cewa shi da jam’iyyarsa za su yi murabus daga majalisar dokokin kasar idan har aka amince da yarjejeniyar, yana mai cewa wannan yarjejeniya za ta kawar da nasarorin da aka samu a yakin da ake yi da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa.
Ben-Gvir ya yi kira da a dakatar da shigar da kayan agaji zuwa Gaza gaba daya domin matsin lamba kan sakin yahudawan shayoniyya da ‘yan gwagwarmaya suka yi garkuwa da su a yankin.