Ministan Tsaron Cikin Gida Na HKI Yace “Yarjeniyar Sulhu Da Hamas” Nasara Ce Gareta

Ministan harkokin cikin gida na HKI Bin-Gafir ya bayyana yarjeniyar sulhu tsakanin HKI da kungiyar Hamas a Gaza nasarace ga kungiyar da sauran Falasdinawa sannan

Ministan harkokin cikin gida na HKI Bin-Gafir ya bayyana yarjeniyar sulhu tsakanin HKI da kungiyar Hamas a Gaza nasarace ga kungiyar da sauran Falasdinawa sannan abin kunya ce ga HKI, don haka idan an aiwatar da wannan sulhun zai sauka daga mukaminsa.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Itamar Ben-Gvir yana fadar haka a jiya Alhamis. Ya kuma kara da cewa tun lokacin da ya ga yadda ake bukukuwa da farin ciki a Gaza da yankin yammacin kogin Jordan ya fahinci wanda ya mika kai.

Ministan ya ce idan an aiwatar da wannan yarjeniyar a ranar Lahadi mai zuwa to zai sauka daga mukaminsa, ba zai sake komawa ba sai an sake komawa yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments