Ministan Lafiya Na Sudan Ya Ce; Yaki Ya Durkusar Da Harkar Kiwon Lafiya A Kasar

Ministan Lafiya na Sudan ya bayyana cewa: Yakin cikin gida ya yi kusan ruguza tsarin kiwon lafiya a kasar Ministan lafiya na kasar Sudan Haitham

Ministan Lafiya na Sudan ya bayyana cewa: Yakin cikin gida ya yi kusan ruguza tsarin kiwon lafiya a kasar

Ministan lafiya na kasar Sudan Haitham Mohamed Ibrahim ya sanar da cewa: Yakin da aka shafe sama da watanni 20 ana gwabzawa a kasar Sudan tsakanin sojoji da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces ya haifar da mummunar barna ga tsarin kiwon lafiya, wanda ya kai ga kusan kammala ruguza shi.

Ma’aikatar lafiya ta kasar ta tattara bayanan mutuwar fararen hula 12,000 a asibitocin kasar, wanda ke wakiltar kashi 10% na adadin wadanda suka mutu a yakin.

A taron manema labarai da ya gudanar a Port Sudan, Ministan Lafiyan kasar ta Sudan ya bayyana cewa: Hasarar da bangaren kiwon lafiya ya yi a sakamakon yakin ya kai kimanin kudi dala biliyan 11. Ya yi nuni da cewa, asibitoci 250 cikin 750 ba su gudanar da aiki saboda barnar da aka yi musu, wanda ya hana miliyoyin mutane samu kulawar kiwon lafiya a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments