Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da mataimakin firai ministan kasar Hadaddiyar daular larabawa, ko (UAE) wato Sheikh Abdullahi bin Zaid da kuma ministan harkokin wajen kasar.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il, Baghaei na fadar haka. Ya kuma kara da cewa Aragchi ya tattauna da jami’an gwamnatin kasar ta UAE kan al-amuran da suka shafi yankin Asiya ta Yamma, musamman dangane da kasar Falasdinu da kasar Siriya,
Labarin ya kara da cewa ministan ya yada zango ne a kasar ta UAE bayan ya kammala ziyarar aiki na kwanaki biyu a kasar Chaina.
A Kasar Chaina dai ministan ya gana da jami’an gwamnatin kasar kan dangantakar tattalin arziki mai kafi dake tsakanin kasashen biyu, da kuma yadda zasu karfafata. Sannan ya gana da sakataren kungiyar EURASIA ta tattalin arziki, wacce Iran ta zama mamba a cikinta a cikin yan kwanakin da suka gabata, a wani taron da aka gudanar a Mosco.