Ministan Harkokin Wajen Iran Zai Ziyarci Siriya Da Turkiyya  

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi zai fara wani ran gadi a yankin daga wannan Lahadin kafin daga bisani ya wuce zuwa Turkiyya. Araghchi,

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi zai fara wani ran gadi a yankin daga wannan Lahadin kafin daga bisani ya wuce zuwa Turkiyya.

Araghchi, zai fara ran-gadin daga kasar Syria a yau, don tattaunawa kan halin da ake ciki musamman a baya bayan nan.

Kafin hakan dama kasar Rasha ta sanar da tattaunawa ta daban da Iran da Turkiyya game da halin da ake ciki na “hadari” a Siriya, game da ‘yan ‘yan ta’adda dake kokarin dannawa wasu yankunan kasar ta Siriya.

Rasha da Iran dai na zaman manyan kawayen gwamnatin Bashar al-Assad.

A yayin wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin manyan jami’an diflomasiyyar Rasha da Turkiyya, bangarorin biyu sun nuna matukar damuwarsu kan halin da ake cioki a Siriya.

A daya bangaren kuma “Ministocin harkokin wajen kasashen Rasha da Iran sun amince da bukatar kara karfafa kokarin hadin gwiwa da nufin daidaita al’amura a Syria,”. Bayan wata tattaunawa da sukayi inji Moscow.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments