Ministan harkokin wajen Iran, ya nufi kasar Sin a wannan Alhamis a wata ziyara mai manufar kyakyata danganta tsakanin kasashen biyu.
Abbas Araghchi, na ziyarar ne a kasar ta Sin, bisa gayyatar da takwaransa ya yi masa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya bayyana cewa “Wannan ita ce ziyarar aiki ta farko da babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya kai wannan kasa tun bayan da sabuwar gwamnatin Iran ta hau kan karagar mulki.”
A yayin wannan ziyara, ana sa ran Araghchi zai tattauna da takwaransa na Sin kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da batutuwan da suka yankin dama batutuwa na kasa da kasa da kuma tsarin aiwatar da cikakken daftarin hadin gwiwa na tsakanin Iran da Sin.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana irin kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Sin a bangarori daban-daban.
Ismail Baghaei ya kara da cewa, ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi a birnin Beijing, za kuma ta bude babi na tuntuba da musayar ra’ayi tsakanin kasashen aminnan juna.