Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Karbi Bakwancin Takwaransa Na Kasar Oman

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya karbi bakwancin takwaransa na kasar Oman a birnin Tehran fadar mulkin kasar ta Iran Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya karbi bakwancin takwaransa na kasar Oman a birnin Tehran fadar mulkin kasar ta Iran

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi ya karbi bakwancin Badar al-Busaidi ministan harkokin wajen masarautar Oman da tawagarsa da suka kawo ziyarar aiki Iran a jiya Litinin.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Ziyarar ministan harkokin wajen kasar Oman dsa tawagarsa a jiya Litinin ta zo ne bisa gayyatar da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi ya yi masa, inda zaman tattaunawan bangarorin biyu zai fi mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi alakar da ke tsakaninsu da kuma ci gaban da ake samu a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ministan harkokin wajen Oman ya kuma shirya ganawa da wasu manyan jami’an siyasa da na tattalin arziki a Iran domin tattaunawa kan muhimmancin bunkasa wadannan fannoni a tsakanin kasashensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments