Ministan harkokin wajen na jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakchi ya isa birnin Damascuss a yau Lahadi, a matsayin zangon farko na ziyarar da ya fara a cikin wannan yankin.
Ziyarar tasa a birnin Damascus tana nufin yin shawarwari akan yanayin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya, da kuma abubuwan da suke faruwa a cikin Syria.
Rahotannin farko da suke fitowa daga kasar Syria, sun ce an yi ganawa a tsakanin Ministan harkokin wajen na Iran da Shugaba Basshar Asad na Syria.
Gabanin barinsa Tehran ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana cewa; Tabbas Iran tana goyon bayan gwamnatin Syria.
Har ila yau, Abbas Arakchi ya ce; Babu wani banbanci a tsakanin HKI da ‘yan Takfiriyyah.