Ministan Harkokin Wajen Cuba Ya Mayar Wa Da Shugaban Kasar Amurka Martani

Bruno Eduardo Rodríguez ya kuma ce; Karairayin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi a MDD ba za su sauya gaskiyar dake kas aba,
cuba,

Ministan harkokin wajen kasar Cuba Bruno Eduardo Rodríguez ya mayar da martani ga shugaban kasar Amurka Donald Trump yana mai cewa; Cuba kas ace mai ‘yanci kuma za ta ci gaba da kasancewa haka.

A jiya Laraba ne dai Ministan harkokin wajen na kasar Cuba Bruno Eduardo Rodríguez ya bayyana cewa; Kasar Amurka ta ki karbar tabbatacciyar gaskiya akan cewa; Cuba kasa ce mai ‘yanci,kuma hakkin wannan kasar ne ta ci gaba da wanzuwa a hakan.”

Bruno Eduardo Rodríguez ya kuma ce; Karairayin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi a MDD ba za su sauya gaskiyar dake kas aba, na kasantuwar Cuba kasa mai cikakken ‘yanci da cin gashin kai.:

Haka nan kuma ya ce; Ko kadan kasar cuba ba ta yin barazana ga tsaron Amurka ko kuma wata kasa ta daban.

Bruno Eduardo Rodríguez ya zargi Amurka da killace kasar da hana shigar da makamashi yana mai cewa; Wannan killacewar ce barazana ga Cuba, kuma tana yin tasiri ga wasu kasashen.

Bugu da kari ministan harkokin wajen kasar ta Cuba ya bayyana matakin na Amurka na kakaba wa kasarsa takunkumi da cewa kisan kiyashi ne da azabtar da al’umma baki daya, kamar yadda ya jaddada cewa kasarsa mai zaman lafiya ce, ta kuma dace da zama cikin zaman lafiya.

Kasar ta cuba dai tana fuskantar takunkuman Amurka masu tsanani musamman akan makamashi, tare da hana shigar da man fetur da baya kasar take samu daga Venezuela.

A dalilin haka ana fuskantar yawan dauke wutar lantarki a cikin Cuba da yake shafar harkokin kiwon lafiya da rayuwar yau da kullum ta mutanen kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted