Ministan cikin gida na kasar Pakistan Sayyid Mohsen Naqavi ya ce ya taho da sako na musamman daga babban kwamandan sojojin kasar Filmasha Munir da kuma Sharif ga jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi Mujtaba Khamanaei.
Prime Minister Shehbaz Sharif, ya aika wa sako ga jagoran juyin juya halin musulunci Ayatollahi Sayyed Mojtaba Khaminaei, dangane da halin da ake ciki.
Tashar talabijan ta Presstv ta nakalto Syed Mohsin Naqvi yana fadar haka jim kadan bayan isowarsa Tehran daga birnin Islamabad. A lokacin ganawarsa da Eskandar Mo’meni tokwaransa na kasar Iran.
Kasar Pakistan ne take shiga tsakani Amurka da Iran tun bayan dakatar da budewa juna wata a yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar, inda a cikinsa suka kashe jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Imam Sayyid Aliyul Khaminaei.
Naqavi ya godewa shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqar Qalibof da kuma ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi on kokarin da suke yi na ganin an kawo karshen halin da ake ciki a wannan yakin.
Dangane da dangantaka tsakanin Iran da Pakistan kuma Naqavi ya zasu tattauna kan yanda zasu kara yawan kasuwanci tsakanin kasashen biyu zuwa dalar Amurka biliyon boyi.