Milyoyin Jama’a na ban kwana da Shahid Ayatollah Seyed Khamenei

Miliyoyin jama’a daga sassa daban daban na Iran da wasu kasashe ketare na ci gaba da taruwa a babban masallacin Tehran a ranar farko ta

Miliyoyin jama’a daga sassa daban daban na Iran da wasu kasashe ketare na ci gaba da taruwa a babban masallacin Tehran a ranar farko ta makoki na ban kwanan karshe da jagoran juyin juya halin Musulunci, Shahid Ayatollah Seyed Ali Khamenei.

Kafofin yada labarai na Iran sun nuno dubban jama’a dauke da hotuna na jagoran mai rasuwa da ma na yanzu da tutocin kasar tare da kiran a dauki fansa.

Kafin hakan a ranar Juma’a, wakilan kasashen waje ne suka isar da tasu ta’aziyyar a hukumance ga Iran.  

Manyan baki ne daga kasashen waje tare da wakilai daga ko’ina cikin Asiya, Afirka, Turai, Amurka, da manyan kungiyoyin kasa da kasa da suka halarci taron.

Tawagar ta kunshi shugabanni, firaministoci, kakakin majalisun dokoki, ministocin harkokin waje, manyan jami’an gwamnati, shugabannin siyasa, da wakilan kungiyoyin addini da kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya, suka halarci tarurukan jana’izar.

Ayatollah Khamenei ya yi shahada a wani harin kawacen Amurka da Isra’ila a Tehran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Kisan sa ya haifar da Allah wadai daga Iran da kawayenta, yayin da miliyoyin ‘yan Iran da kungiyoyin gwagwarmaya a fadin yankin suka yi jimamin shahadarsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted