MDD ta yi maraba da yarjejeniyar Iran da IAEA dangane da komawa bincike

Stéphane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana a jiya Laraba cewa, MDD ta yi maraba da yarjejeniyar da Iran ta kulla da hukumar kula

Stéphane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana a jiya Laraba cewa, MDD ta yi maraba da yarjejeniyar da Iran ta kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA, kan “tsarin da zai ba da damar komawa bincike a Iran”.

A yayin taron manema labarai a wannan rana, Dujarric ya ce wannan yarjejeniya wani mataki ne mai kyau da Iran da IAEA suka dauka don komawa cikakkiyar hadin gwiwa. Majalisar tana kuma fatan za a gaggauta aiwatar da yarjejeniyar.

Dujarric ya kuma jaddada muhimmancin cikakkiyar hadin gwiwar Iran da IAEA. Yana mai cewa, hakan yana da muhimmanci wajen kafa wani tsari na dogon lokaci, wanda zai “tabbatar da shirin nukiliyar Iran gaba daya don zaman lafiya”.

A ranar Larabar, yayin ziyararsa a Alkahira, babban birnin kasar Masar, ministan harkokin wajen Iran Abass Araghchi, ya sanar da cewa, Iran ta kulla yarjejeniya da IAEA don sake yin hadin gwiwa tsakaninsu kan batun nukiliyar Iran.

Iran ta dakatar da hadin gwiwa da IAEA, bayan harin da Isra’ila da Amurka suka kaddamar kanta a watan Yunin bana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments