Kwamitin tsaron MDD ya kira yi kasar Rwanda da ta janye sojojinta daga gabashin kasar DRC, haka nan kuma ta tsawaita aikin dakarun majalisar na zaman lafiya na tsawon shekara daya.
A zaman da kwamitin tsaro na MDD ya yi a ranar Juma’ar da ta gabata ya yi Allawadai da harin na kungiyar ‘yan tawaye ta M23 wacce kasar Rwanda take goyawa baya. Haka nan kuma Kwamitin ya yi kira ga kasar ta Rwanda da ta dakatar da taimakon da take bai wa kungiyar ‘yan tawayen da kuma janye nata sojojin.
Da akwai rundunar tabbatar da zaman lafiya ta MDD a kasar Congo ” MONUSCO” mai sojoji 11,500, wacce kuma a yanzu aka kara tsawon aikinsu na sheara guda.
Wannan kiran dai ya zo ne bayan da kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 ta riya cewa ta janye daga garin Uvira da ta shiga a karshen makon da ya shude.
Sai dai gwamnatin kasar ta DRC ta ce har yanzu M23 ba ta fice daga cikin garin na Uvira ba.
Mataimakiyar jakadan Amurka a MDD Jennifer Locetta ta fada wa kwamitin tsaro cewa dole ne mayakan na M23 su fice daga cikin garin Uvira.
Amurka dai tana shiga cikin batun DRC ne saboda bukatuwarta da ma’adanan da Allah ya huwace wa wannan kasa masu kima da daraja.