Kungiyar Dakarun Kai Daukin Gaggawa ( RSF) ta kasar Sudan ta sanar da kwace iko da birnin El-Fashar, da nan ne tungarta ta karshe a yankin Darfur. Hakan dai ya haddasa matsalar dangane da ayyukan jin kai da ceto saboda yadda aka rutsa da dudun mutane a cikin birnin.
A jiya Litinin ne dai rundunar ta (RSF) ta kame wani sansanin soja mai matukar muhimmanci a Arewacin babban birnin na yankin Darfur.
Garin El-Fasha ne dai sansani mafi girma da sojojin kasar Sudan suke iko da shi a yankin Darfur.
Wani rahoton MDD ya ambaci cewa da akwai fiye da mutane 26,000 da suke a tarwatse a cikin birnin na Darfur a tsawon shekara daya da aka dauka ana killace da birnin.
Jami’ia MDD mai kula da ayyukan agaji da ceto a Sudan Denis Brown ta yi kiran gaggawa ga mayakan na RSF da su kyale mutanen garin su fice zuwa inda suke so.
Denis Brown ta ce da akwai bukatar a girmama dokokin kasa da kasa na kyale mutane su fita.
A gefe daya, jami’an kiwon lafiya sun sanar da mutuwar fararen hula masu yawa sanadiyyar lalata cibiyoyin kiwon lafiya da yaki ya yi.