Babban sakataren MDD, Antonio Guterres ya yi gargadi a jiya juma’a da safe, akan abinda ya kira ‘yanayi mai cike da damuwa da yake faruwa a cikin kasar Sudan ta Kudu.
An sami tashin hankali da fadace-fadace a cikin kasar ta Sudan ta kudu a ranar Laraba da jami’an tsaro su ka yi wa mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar daurin talala a cikin gidansa.
Babban magatakardar MDD ya yi kira ga ‘yan siyasar kasar ta Sudan ta Kudu da su ci gaba da riko da yarjejeniyar sulhu da zaman lafiya,inda ya ce: “ A dawo da gwamnatin hadin kan kasa, da aiki da alkawullan da aka yin a zaman lafiya da sulhu, da hakan ne kadai hanyar dawo da zaman lafiya da kuma yin zabe a cikin watan Disamba 2026.”
A halin da ake ciki a yanzu, kungiyar tarayyar Afirka tana aikin hadin gwiwa da MDD domin kawo karshen dambaruwar siyasar da ake ciki a kasar.”
Gutrres ya ce; Muna goyon bayan tarayyar Afirka na aikewa da tawagar dattijan nahiyar zuwa Afirka ta kudu da kuma wata tawagar a karkashin jagorancin shugaban kasar Kenya Ruto.
Babban sakataren MDD ya kira yi shugabannin kasar ta Sudan Ta Kudu das u ajiye makamansu na yaki, su kuma bai wa al’ummar kasar fifiko.