Saudiyya ta sanar da hango watan Shawwal, ranar lahadi ce Sallah a kasar

Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da hango jinjirin watan Shawwal, wanda ke nufin kawo karshen watan azumin Ramadana. Shafin Haramain ne ya ruwaito hakan, bayan daukar awanni ana neman wata. Wannan ke nufin gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal, wato ranar karamar Sallah a kasar ta Saudiyya.

Hamas ta yi Tir da kakkausar murya da harin Isra’ila kan masu aikin ceto a Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan kungiyoyin kare fararen hula da masu aikin ceto Palasdinawa a Rafah da ke kudancin zirin Gaza, tare da bayyana hakan da aikata laifukan yaki. Sojojin Isra’ila sun amince a ranar Asabar 29 ga watan Maris cewa […]

Najeriya : An samu hargitsi a yayin jerin gwanon ranar Kudus a Abuja

Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane 20 ne suka mutu sakamakon hatsaniyar da aka samu tsakanin sojoji da masu jerin gwanon ranar Kudus ta duniya a Abuja fadar mukin Najeriya. Hotunan faifan bidiyo sun nuna yadda masu zanga-zangar ke neman mafaka yayin da karar harbe-harbe ke kara kamari a kusa da su. An ce an […]

Adadin mamata a girgizar kasar Myanmar ya ka 1,644

Hukumomi a Myanmar sun ce adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar ya kai 1,644, yayin da wasu 3,408 suka jikkata, ye zuwa ranar Asabar din nan. Tunda farko dai mutane 1,007 ne aka sanar sun mutu sai wasu 2,389 da suka jikkata. Girgizar mai karfi maki 7.7 ta shafi Kasashen Myanmar da Thailand wadanda […]

Mai Bawa Jagora Shawara Ya Ce ‘Wa’adussadik Na III” Na Kan HKI Na Hanya

Wani babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa hare-haren ‘WaaduSsadik na III’ don maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kaiwa Iran a shekarar da ta gabata suna kan hanya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar […]

Kwamandan IRGC Ya Gargadi Amurka Dangane Da Hari Kan Kasar A Ranar Qudus Ta Duniya

Kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC Rear Admiral Ali-Reza Tangsiri ya tunatar da gwamnatin Amurka kan cewa idan ta aikata wawta ta kaiwa cibiyoyin Nukliyar kasar zata gamu da maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Tansiri yana fadar haka a kan jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki […]

Kungiyar “White Helmets Ta” A Kasar Siriya Ta Rasha Tallafin Da Take Samu Daga USAID

Kungiyar bada agajin ta gaggauwa ta “white Helmets” na kungiyar Al’kaida, wacce kuma take samun tallafin gwamnatin Amurka ta hukumar USAID ta rasa tallafin da take don gudanar da ayyukanta. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana cewa, kasashen yamma musamman Amurka sun yi amfani da kungiyar ta Al-qaeda a lokacin yakin kasar […]

MDD Ta Yi Gargadi Akan Mummunan Yanayin A Sudan Ta Kudu

babban sakataren MDD

Babban sakataren MDD, Antonio Guterres ya yi gargadi a jiya juma’a da safe, akan abinda ya kira ‘yanayi mai  cike da damuwa da yake faruwa a cikin kasar Sudan ta Kudu. An sami tashin hankali da fadace-fadace a cikin kasar ta Sudan ta kudu a ranar Laraba da jami’an tsaro su ka yi wa mataimakin […]

Maduro Ya Bayyana Sakataren Harkokin Wajen Amurka Da Cewa Wawa Ne

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da yake ziyarar aiki a kasar Guyana da cewa, sakarai ne. A yayin ziyarar da sakataren na  harkokin wajen Amurka ya kai zuwa kasar Guyana mai makwabtaka da Venezuela, ya ce, Amurka za ta mayar da martani mai karfi akan Venezuela idan […]

 Iran Ta Yi Allawadai Da Sabon Harin HKI A Kasar Lebanon

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakinta Dr. Isma’ila Baka’i, ta yi tir da sabbin hare-haren da HKI ta kai wa kasar Lebanon a daidai lokacin da ake bikin ranar Kudus. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na kasar ta Iran ya bayyana cewa; Abinda HKI ta yi keta tsagaita wutar yaki ne,wanda abin a yi tir […]

Sharhi: Taruka Da Gangamin Ranar Quds Ta Duniya 2025

A wannan Juma’a ce 28 ga watan Maris na shekarar 2025, aka gudanar da taruka da jerin wano na ranar Qudus ta duniya wadda ta zo daidai da ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma. An gudanar da wadannan taruka da jerin gwano ne a kasashe daban-daban da suka hada da wasu kasashen musulmi […]