MDD Ta Yi Allah-wadai Da Hare-haren Isra’ila Kan Asibitoci A Gaza

Wani sabon rahoto da ofishin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar ya ce hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kai

Wani sabon rahoto da ofishin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar ya ce hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kai wa asibitoci a Gaza ya yi mummunar illa ga tsarin kiwon lafiya na yankin.

Jeremy Laurence, kakakin ofishin hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya OHCHR, ya ce a ranar Talata gwamnatin kasar ta yi amfani da manyan bama-bamai wajen kai hari kan fararen hula dake samun mafaka a asibitoci.

Laurence ya kara da cewa ofishin na MDD ya kuma tabbatar da sahihancin harin da aka yi wa mutanen da ke cikin asibitoci, ciki har da ma’aikatan kiwon lafiya.

Ya jaddada cewa kai hare-hare da gangan a wuraren da ake jinyar marasa lafiya da wadanda suka jikkata laifi ne na yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments