Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa ta samu wasikar bukatar Amurka ta ficewa daga Hukumar Lafiya ta Duniya a shekarar 2026, kamar yadda Shugaba Trump ya umarta ranarsa ta farko ta hawa karagar mulki.
Amurka za ta fice a hukumance daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a watan Janairun 2026 bayan da hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta samu wata wasika ta musamman daga Trump a wannan makon, inji mataimakin mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya Farhan Haq.
“Zan iya tabbatar da cewa yanzu mun sami wasikar Amurka kan janyewa daga WHO wanda Zai fara aiki daga ranar 22 ga Janairu 2026, “in ji Haq.
Trump ya kuma umarci gwamnatinsa da ta “dakatar da mika duk wasu kudade, tallafi, na gwamnatin Amurka a nan gaba ga hukumar ta WHO”.
Washington ta kuma bukaci dukkan jami’an gwamnatin da ke aiki tare da WHO da su daina shiga muhawarori ko tattaunawa da WHO ke jagoranta kan tinkarar cututuka.
Amurka tana ba da gudummawar kusan kashi 18 cikin 100 na kudaden hukumar, sai kasar China dake biye ma ta a matsayi ta biyu.
Masana da dama na ganin ficewar Amurka daga hukumar ta WHO, zai yi tasiri ga hukumar wajen tunkarar ayyukan yaki da manyan cutuka musamman irinsu tarin fuka da cutar kanjamau.
Trump ya zargi hukumar ta WHO da nuna fifiko lokacin bullar cutar korona (COVID-19) a lokacin wa’adinsa na farko a kan karagar mulki kuma ya aike da bukatar ficewa daga kungiyar a watan Yulin 2020, saidai
Wannan yunkurin ya ci tura lokacin da ya sha kaye a zaben shugaban kasa na 2020 a hannun Joe Biden.