MDD Ta Nuna Damuwarta Akan Mutuwar Jariran Gaza Saboda Sanyi

Mai Magana da yawun MDD Stephane Dujarric ya fada wa manema labaru cewa; Ofishin dake kula da ayyukan jin kai a Gaza ya fada mana

Mai Magana da yawun MDD Stephane Dujarric ya fada wa manema labaru cewa; Ofishin dake kula da ayyukan jin kai a Gaza ya fada mana sun shiga cikin damuwa mai zurfi akan mutuwar jaririn da bai wuce wata daya da haihuwa ba saboda sanyi. Wannan shi ne abinda ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana mana. Kuma wannan shi ne yaro na takwas da ya rasu saboda tsananin sanyi a cikin kasa da makwanni uku.”

Har ila yau ya kara da cewa; Abu ne mai yiyuwa a iya hana afkuwar wannan irin mutuwar, idan ace an samar wa da iyayensu kayan da za su ba su kariya.

Bugu da kari Dujarric ya ce hukumar agajin ta MDD tana cigaba da karbar rahotanni akan yadda ake kashe fararen hula a cikin yankin na Gaza, tare da kuma da haddasa barna mai girma.

Haka nan kuma ya yi ishara da yadda Isra’ila take kai wa makarantun MDD hare-hare,sannan ya ce; Wajibi ne a bayar da kariya ga farafen hula da kuma cibiyoyin da fararen hula suke amfani da su, da kuma kayan agaji,kamar yadda yake a karkashin MDD.

Falasdinawa ‘yan gudun hijira dai suna rayuwa ne a cikin hemomin da aka yi da leda da kuma yadi adaidai lokacin da ruwa kamar da bakin kwarya yake sauka, ga shi kuma ba su da bargunan lullube jikinsu, kuma kasar da suke kwance a kanta ta jike.

Da akwai Falasdinawa miliyan biyu da suke rayuwar hijira alhali adadinsu baki daya bai wuce miliyan biyu da dubu dari hudu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments