Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta yi gargadi akan fadan kabilanci da ya barke a yankin al’jazirah da hakan zai kara dagula halin da kasar ta Sudan take ciki.
Mai Magana da yawun hukumar kare hakkin bil’adama din ta MDD Ravina Shamdasani ta kara da cewa: Yanayin da fararen hula suke ciki a Sudan yana kara tabarbarewa bayan rahotannin da suke nuni da cewa an sami barkewar fadan kabilanci a gabashin jahar Aljazira.”
Shamdasani ta yi kira a jiya Juma’a daga birnin Geneva ga shugaban majalisar rikon kwarya, da kuma kwamandan rundunar kai daukin gaggawa da su gaggauta tsagaita wutar yaki.
A wani rahoton daga kasar ta Sudan an kai wani hari da jirgin sama maras matuki a ranar 13 ga watan Janairu akan garin Omdurman, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar fararen hula 120, da kuma wasu 150 da su ka jikkata.