Hukumar kula da jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ta nuna damuwa kan yadda Isra’ila ke toshe hanyoyin kai agaji a Gaza, kamar yadda kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC) ta yi gargadin cewa hakan na jefa fararen hula a cikin wani mummunan yanayi.
OCHA ta fada cewa hukumomin Isra’ila sun hana agaji sama da 150 shiga Arewacin Gaza tun watan Oktoba.
Asibitin Kamal Adwan yanzu ba ya aiki, biyo bayan wani farmaki da Isra’ila ta kai ranar Juma’a wanda ya tilasta aka kwashe marasa lafiya da ma’aikatan asibitin.
A cikin kwanaki uku da suka gabata, a cewar OCHA, sama da kashi 60 cikin 100 na kungiyoyi 42 na Majalisar Dinkin Duniya an hana su gudanar da aikinsu ko kuma shiga cikin Gaza.
Har ila yau ICRC a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin ta yi gargadin cewa hare-haren da Isra’ila ta kai kan asibitoci sun “rushe” tsarin kula da lafiya a Arewacin Gaza.