MDD ta bada sanarwan cewa hana shigowar kayakin agaji ne ya sa Falasdinawa a zirin Gaza basa samun abinci da tantuna wadanda zasu taimaka wajeb kyautata rayuwar mutanen yankin.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterre Stephane Dujarric yana fadar haka. Ya kumakara da cewa, Falasdinawa a Gaza sun ci gaba da kasancewa a cikin wannan mummunan halin ne, saboda hana shigarda kayakin agaji, wadanda suka hada da abinci da kuma tentuna zuwa kashi 65% na yankin Gaza ne yasa falasdinawa a yankin suke irin wannan mummunan rayuwa.
Dujarrec ya kara da cewa sauyan kashi 35% na zirin Gaza yana cike da falasdinawa har ya wuce yanda ya dace. Kakakin Gottertess ya bayyana haka ne a jiya Laraba ga kafafen watsa labarai a helkwatan MDD a birnin NewYorka ya kuma kara da cewa, a halin yanzu mafi yawan Falasdinawa suna zaune ne a wuri mai kunci a gazar, kuma suna cikin mummunan hali, musamman a lokacinda sanyi da ruwan sama yake shigowa.
Yace majalisar tana tunanin samar da hanyoyin kare Falasdinawa a Gaza daga sanyin hunturun da ruwan saman da ke karatowa. Ya ce a halin yanzu jami’an majalisar suna aikin gano yanda zasu tallafawa sansanonin yan gudun hijira 450 wadanda sojojin HKI suka tilastawa zama a wuraren basu dace ba, kuma suna iya fuskantar ambaliyar ruwa a cikin wannan lokacin sanyi mai zuwa. Yawan Falasdinawa da suke fama da wannan matsalar sun kai kashi 20 % a zirin Gaza.