MDD Ta Bukaci Isra’ila Ta Gaggauta Ficewa Daga Lebanon

Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci Isra’ila data fice daga yankin Lebanon ba tare da wani bata lokaci ba. Mataimakin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya kan

Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci Isra’ila data fice daga yankin Lebanon ba tare da wani bata lokaci ba.

Mataimakin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya kan ayyukan wanzar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix ya ce tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Hizbullah na da rauni, yana mai kira ga sojojin Isra’ila da su janye daga yankunan kudancin Lebanon.

M. Lacroix ya shaida wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya Ya ce tura sojojin Lebanon zuwa kudanci ya dogara ne kan janye sojojin Isra’ila.

“A kwanaki 60 da aka ayyana na janye sojojin Isra’ila daga Lebanon, duk da haka, Isra’ila ta ci gaba da rusa gine-gine, da filayen noma,” in ji shi.

“An kuma bayar da rahoton wasu hare-hare ta sama, kamar yadda ake ci gaba da keta haddin sararin samaniyar Lebanon,” in ji shi.

Babban jami’in na Majalisar Dinkin Duniya ya ce mamayar da sojojin Isra’ila ke ci gaba da yi, saba wa kuduri mai lamba 1701 ne na kwamitin sulhu, wanda ya samar da tsagaita wuta a yakin da gwamnatin Tel Aviv ta kaddamar da kasar Lebanon a shekara ta 2006.

Yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta fara aiki ne a ranar 27 ga watan Nuwamba 2024.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments