Majalisar Dinkin Duniya ta bakin Jami’ar Musamman kan yanayin kare hakkin dan adam a yankunan Falasdinawa da aka mamaye ta bayyana damuwarta kan ayyukan “ta’addanci” da ake yi a kullum kan Falasdinawa, tana kira ga Tarayyar Turai da ta dauki mataki kan “wariyar launin fata da Isra’ila ke yi.”
Francesca Albanese ta yi tsakaci ne game da karuwar tashin hankalin da yahudawa ‘yan kama wuri zauna ke yi wa Falasdinawa a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
“Na yi mamakin rashin daukar mataki na siyasa akan abin da ake yi a Falasdinu, inda ta’addanci ke karuwa a kullum,” in ji Ms. Albanese a wani sako a shafinta na Twitter.
“A Yammacin Kogin Jordan, ana kona bishiyoyi kuma ana sanya guba ga dabbobi,” inji ta.
Ta kara aza ayar tambaya: tana mai cewa “Yaushe Tarayyar Turai za ta dauki mataki kan wariyar launin fata ta Isra’ila?”
Kimanin ‘yan gudun hijira 750,000 suna zaune a matsugunan da ba a ba su izini ba a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, ciki har da kimanin 250,000 a Gabashin Kudus da aka mamaye.
Tun lokacin da Isra’ila ta fara yakin kisan kare dangi a yankin Gaza a watan Oktoban 2023, Yammacin Kogin Jordan ya fuskanci ayyukan sojojin Isra’ila da tashin hankalin mazauna yankin ‘yan kama wuri zamna.
Wadannan hare-haren sun haifar da mutuwar dubban mutane da kuma sace dubban Falasdinawa.
Ana sukar kasashen Yamma sosai saboda rashin daukar mataki a kan kisan kare dangi da aka yi a Gaza da kuma tashin hankalin da yahdawa ‘yan kama wuri zauna ke wa falasdinawa a yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye suka yi.