MDD ta amince da kudurin da ke neman Isra’ila ta bada damar shigar da agaji a Gaza   

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wani daftarin kuduri da ke neman Isra’ila ta bada damar shigar da agajin jin kai ba tare da wani

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wani daftarin kuduri da ke neman Isra’ila ta bada damar shigar da agajin jin kai ba tare da wani sharadi ba zuwa Zirin Gaza.

Kudurin da aka zartar a ranar Juma’a, ya yi kira ga Isra’ila da ta kare cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya tare da bin dokokin kasa da kasa.

An gabatar da wannan matakin ne a matsayin martani ga ra’ayin da Kotun Duniya ta ICJ, ta bayar ga Isra’ila.

Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a tsakanin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da Isra’ila, wacce ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba, 2025, ta wajabta wa Isra’ila bude iyakoki domin ba da damar shigar da abinci, mai, da kayayyakin jin kai ba tare da wani sharadi ba zuwa zirin na Gaza.

Duk da haka Isra’ila ta yi watsi da wadannan alkawuran, inda ta bada damar jigilar kayaki kaɗan zuwa yankin da yakin shekaru biyu ya daidaita.

Tun daga watan Oktoba na 2023, sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa kusan 70,400, yawancinsu mata da yara, tare da raunata wasu 171,000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted