Wani rahoto da MDD ta fitar a ranar Alhamis din da ta gabata ya kunshi cewa, rundunar kai daukin gaggawa, ( RSF) ta kashe fararen hula 1,000 a sansanin ‘yan hajara na Zamzam dake yankin Darfur a cikin watan Aprilu na wannan shekarar ta 2025.
Rahoton dai yana a matsayin wani sabon zargi ne ga rundunar ta (RSF) akan take hakkin bil’adama, bayan wasu jerin zarge-zaregen da aka yi mata a yankuna mabanbanta na Darfur.
Rudunar dai ta kai wancan harin ne a sansanin ‘yan hijira na Zamzam a lokacin da take kokarin kwace iko da birnin Al-Fasha babbn birnin Darfur ta Arewa.
Daruruwan fararen hula ne dai rundunar ta yi wa kisan kiyashi, tare kuma da cin zarafin mata da dama.
Sansanin Zamzan ne mafi girma da ‘yan hijira suke da mafaka da mutane fiye da rabin miliyan a cikinsa. Rundunar RSF ta killace shi ta hana shigar da kayan agaji na tsawon watanni da hakan ya jefa mutane cikin yunwa da wahalhalu.